Dsa Ameer 420

Dsa Ameer 420 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dsa Ameer 420, Nassarawa, Kano.

10/05/2026

Alhamdulillah

Mai yasa wasu yan takarar ake jifan su,Adawa? Ko kiyayya?
09/05/2026

Mai yasa wasu yan takarar ake jifan su,
Adawa? Ko kiyayya?

09/05/2026

Sirrin amarya

Maxajan da suke auran mata hudu basa tsoran wataran ta kiskure su hada kai suyi masa dukan tsiya 🤕
07/05/2026

Maxajan da suke auran mata hudu basa tsoran wataran ta kiskure su hada kai suyi masa dukan tsiya 🤕

Rayuwarmu ta yau muna cikin matsala b***e ta gobe Tinubu yacire tallafi a kan mai PMS, LPG da AGO, amma ya bayar da umar...
03/05/2026

Rayuwarmu ta yau muna cikin matsala b***e ta gobe
Tinubu yacire tallafi a kan mai PMS, LPG da AGO, amma ya bayar da umarnin tallafin man jirgin sama.
Gwamnatin masu hannu da shuni kenan! Kana talaka kana rigima wajen biyan kudin Keke Napep amma kana goyon bayansu 😂😁

01/05/2026

Good night coming soon

Yaudara Phone Store 😂😂HONOURABLE Ya Futo Neman Quri"ar Talakawa.😜Kafin Yaci Ya Gudu Yabar Ku Da Rabon Kwana Shinkafa Da ...
01/05/2026

Yaudara Phone Store 😂😂
HONOURABLE Ya Futo Neman Quri"ar Talakawa.😜Kafin Yaci Ya Gudu Yabar Ku Da Rabon Kwana Shinkafa Da Taliya Leda 1🤣🙏

HATSARI GOMA SHA DAYA: Abubuwan Da Zasu Faru Da 'Yan Arewa Idan Gwamnatin Tinubu Ta Sake ZarcewaAl'ummar Arewa, lokaci y...
27/04/2026

HATSARI GOMA SHA DAYA:
Abubuwan Da Zasu Faru Da 'Yan Arewa Idan Gwamnatin Tinubu Ta Sake Zarcewa
Al'ummar Arewa, lokaci ya yi da zamu duba halin da muke ciki da kuma inda aka dosa. Idan muka yi kuskuren barin wannan gwamnati ta ci gaba da jan ragamar kasar nan bayan wa'adinta na farko, ga wasu daga cikin manyan matsalolin da ka iya dabaibaye yankinmu

▪️1. Kara Tabarbarewar Tsaro
Idan aka ci gaba da salon tafiyar yanzu, akwai fargabar cewa garkuwa da mutane da ta'addanci zasu zama ruwan dare, ganin yadda yankinmu ya zama fagen fama ba tare da gagarumin sauyi ba.

▪️2. Mutuwar Tattalin Arzikin Arewa
Manufofin tattalin arziki na yanzu sun riga sun jefa kananan sana'o'i da dama cikin garari. Kara tazarce na nufin karuwar fatara da talauci ga talakan Arewa.

▪️3. Karuwar Rushewar Farashin Abinci
Arewa ita ce rumbun abincin Najeriya, amma tsadar taki, man fetur, da rashin tsaro a gonaki na barazana ga rayuwar kowa. Idan ba a samu canji ba, yunwa na iya zama babban kalubale.

▪️4. Mayar da Arewa Saniyar Ware
Akwai fargabar cewa za a ci gaba da nuna wariyar launin fata a bangaren nade-naden mukamai da ayyukan raya kasa, inda za a bar Arewa a baya wajen manyan ayyukan gwamnatin tarayya.

▪️5. Rugujewar Ilimi
Tsadar karatun jami'a da sauran makarantun gaba da sakandare na nufin dubban matasan Arewa zasu bar makaranta, wanda hakan zai haifar da karuwar rashin aikin yi da shiga ayyukan assha.

▪️6. Rashin Kulawa da Ma'aikatan Gwamnati.
Rage darajar naira da hauhawar farashin kaya sun sa albashin ma'aikaci ya zama ba shi da amfani. Ci gaba da wannan tsari zai ruguza jin dadin ma'aikata a yankinmu.

▪️7. Karewar Tasirin Siyasar Arewa
Idan Arewa ba ta nuna fin karfinta a zabe mai zuwa ba, za a daina daukar yankin a matsayin mai fada aji a harkar siyasar Najeriya, wanda hakan zai rage mana daraja.

▪️8. Matsalolin Noma da Kiwo
Rashin tsayayyen tsari na magance rikicin manoma da makiyaya zai kara raba mutane da gidajensu, wanda hakan zai shafi karkara da biranen Arewa baki daya.

▪️9. Kuncin Rayuwa na Shura-da-Gaba
Manufofin cire tallafi ba tare da tsarin rage radadi na gaskiya ba zai sa rayuwa ta yi kunci fiye da yadda ake ciki yanzu.

▪️10. Rashin Madogara ga Matasa
Ba tare da sabbin masana'antu ko tallafin kasuwanci ba, matasan Arewa zasu rasa kwarin gwiwar gina kansu, wanda hakan zai haifar da rashin tabbas a nan gaba.

▪️11. Barazanar Raba Kasa da Manufofin Bangaranci.
Idan aka bar wannan gwamnati ta ci gaba, akwai babban hadari na dawowar maganganun raba kasa da tunzura bangaranci.
Salon mulkin da aka nuna na nuna fifiko ga wani bangare da kuma yin biris da bukatun Arewa na iya sa wasu su rika ganin kamar Arewa ba ta da sauran hurumi a cikin kasar, wanda hakan zai iya raunana hadin kan Najeriya da kuma jefa yankinmu cikin rashin tabbas na siyasa da tattalin arziki.

👉Kira ga Al'ummar Arewa:
'Yan uwa, kada mu bari kuskuren baya ya maimaita kansa. Wannan ba batun siyasa ba ne kawai, batun rayuwarmu ne da ta 'ya'yanmu. Dole ne mu tashi tsaye, mu hada kai, mu kuma tabbatar mun zabi shugabancin da zai kalli Arewa da idon rahama, ba wulakanci ba.

👉Lokaci ya yi da zamu ce "A'a" ga tazarce! Mu kare mutuncinmu da rayuwarmu.

27/04/2026

Iya kudinka iya shagalin ka

DUK YADDA KA MATSU DA AURE KADA KA AURI😐😐YARINYAR DA TA FITO A IRIN GIDAJE GUDA 7DINNAN.Aure makaranta ne. Masana halayy...
27/04/2026

DUK YADDA KA MATSU DA AURE KADA KA AURI😐😐
YARINYAR DA TA FITO A IRIN GIDAJE GUDA 7
DINNAN.

Aure makaranta ne. Masana halayyar dan adam sun tabbatar da cewa kowane yaro yana ɗaukar kashi 70% na ɗabi'un da ya tashi ya ga ana yi a gidansu

1. Gidan Da Uwa Take Juya Uba:

2. Gidan Gasar Rayuwar Karya:

3. Gidan Da Saki Bai Zama Abin Kunya Ba:.

4. Gidan Da Babu Sirri (Gidan Surutu):

5. Gidan Da Ake ƙyamar Talaka:

6. Gidan Tsibbu Da Shirka:

Kusaka mana na (7) a Comment section 👇👇👇

Address

Nassarawa
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dsa Ameer 420 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share